A wani sabon salo da ya girgiza fagen siyasa da tsaro a Nijeriya, Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta kama tsohon Ministan Shari’a kuma Lauyan Gwamnatin Tarayya, Malam Abubakar Malami (SAN), domin yi masa tambayoyi kan zargin hannu a harkar tallafa wa ta’addanci, lamarin da ya jawo hankalin jama’a da kafafen yaɗa labarai.
Majiyoyi na tsaro sun ce an kama Malami a Abuja kusa da gidan gyaran hali na Kuje, jim kaɗan bayan ya cika sharuɗɗan beli a wata shari’ar zargin satar kuɗi Naira biliyan 8 da EFCC ke yi masa.
An ce binciken EFCC ya gano makamai a gidansa da ke Birnin Kebbi, inda aka miƙa su ga DSS domin zurfafa bincike kan zargin tallafa wa ta’addanci.
Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa DSS ce ke da alhakin binciken irin waɗannan laifuka, yayin da aka ce wani tsohon minista da ke da alaƙa da lamarin yana waje ƙasar, kuma an saka shi cikin jerin mutanen da ake sa ido a kansu.














